Sayyid Nasrallah Ya Ce Yahudawan Sahayoniyya Su Yi Dariya Kadan Sannan Zasu Yi Kuka Mai Yawa Nan Gaba

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya su yi murna na lokaci kadan amma zasu yi kuka mai yawa nan

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya su yi murna na lokaci kadan amma zasu yi kuka mai yawa nan gaba

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sayyed Hassan Nasrallah ya jaddada cewa: Matakin da suka dauka na mayar da martani kan muggan laifukan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na baya-bayan nan, tabbatattu ne ba su bukatar gudanar da muhawara, kuma dole ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da masu goya mata baya su jira martanin da zai biyo baya. Har ila yau, Sayyid Nasrallah ya musanta alhakin ‘yan gwagwarmaya kan batun Majdal Shams, lamarin da ke nuni da cewa zargin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi kan ‘yan gwagwarmaya akwai mummunar manufa da mugun nufi. A jawabin da ya gabatar a wajen bikin tunawa da shahidi Fouad Shukr da kungiyar Hizbullah ta gudanar a yankin kudancin birnin Beirut Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewa: Manufar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ita ce neman kafar kai farmakin wuce gona da iri kan yankin kudancin kasar Lebanon, don aiwatar da kisan gilla kan babban jagoran mujahidai Sayyid Fouad Shukr -da ake masa lakabi da Sayyid Muhsin-, ya kuma kara da cewa: ‘Yan mamayar yahudawan sahayoniyya sun kuma kai hari kan wani ginin fararen hula da suke zaune a Haret Hareik a yankin kudancin kasar, wanda ya kai ga shahadar mutane 7 da suka hada da mata 3 da yara 2, da wani shahidi daga ‘yan uwa Iraniyawa da kuma shahidi kwamanda Fouad Shukr, da kuma wasu da dama da suka samu raunuka, yawancinsu mata da kananan yara, wasu daga cikinsu har yanzu suna kwance a asibitoci.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments