Sayyed Safieddine: Hizbullah Za Ta Rubanya Hare-Harenta Kan Isra’ila

Shugaban Majalisar Zartarwar Hizbullah ya yi wa Isra’ila kashedin cewa, ta kwana sanin cewa ayyukan da kungiyar ke kaddamarwa na soji za su karu ta

Shugaban Majalisar Zartarwar Hizbullah ya yi wa Isra’ila kashedin cewa, ta kwana sanin cewa ayyukan da kungiyar ke kaddamarwa na soji za su karu ta hanyoyi da yawa.

Dubban jama’a ne suka hallara a yankin kudancin birnin Beirut a yau  Laraba domin janazar wani babban kusa na kungiyar Hizbullah Taleb Sami Abdallah (Abu Taleb), wanda ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a yammacin jiya Talata a Jwaya. kudancin Lebanon.

A jawabin da ya gabatar a wurin taron, shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sayyed Hashem Safieddine ya jaddada cewa yahudawan sahyuniya ba su koyi darasi daga abubuwan da suka faru a baya ba na yakin da suka yi da Hizbullah.

“Isra’ila ta dage da wautar ta… tana ganin cewa kashe shugabanni gwagwarmaya  zai raunana su ” in ji shi, yana mai nuni da cewa kwarewa ta nuna cewa Hizbullah tana kara karfi ne kawai kuma yana kara tsayin daka bayan shahadar shugabanninta.

Sayyed Safieddine ya jaddada cewa “dole ne Isra’ila ta fahimci” cewa matakin da Hezbollah za ta dauka shi ne kara kai hare-hare a zirin Gaza, “a iri da yawa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments