Rukunin Farko Na Jami’an Tsaron Kenya Sun Isa Haiti Don Tabbatar Da Tsaro

Bayanai daga Kenya na nuni da cewa rukunin farko na jami’an tsaron kasar da zasu tafi Haiti don tabbatar da tsaro sun kama hanya. Shugaban

Bayanai daga Kenya na nuni da cewa rukunin farko na jami’an tsaron kasar da zasu tafi Haiti don tabbatar da tsaro sun kama hanya.

Shugaban kasar William Ruto ya gudanar da wani takaitaccen biki a ranar Litinin ga bataliya ta farko zuwa kasar Haiti, wadda ta tashi daga Nairobi zuwa Port-au-Prince.

 Tun a watan Oktoba, Kenya ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya don tabbatar da aikin tsaro a tsibirin Caribbean, domin yakar kungiyoyin masu dauke da makamai wadanda ke rike da kashi 80% na babban birnin kasar Haiti.

Daga cikin jami’an tsaro 1,000 da kasar dake gabashin Afirka za ta tura, rukunin farko ya shafi ma’aikata 400 da aka dauka aiki.

Tawagar ta MMAS, wanda aka shirya aikinta na tsawon shekara guda zuwa Oktoba 2024, na samun dauki Benin, Chadi, da Bangladesh, Bahamas da Barbados.

Tun daga watan Oktoban 2023, Kenya ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya don gudanar da aikin.

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya kuma tunatar da mutanensa game da muhimmancin “mutunta hakkin bil’adama” a wannan babban aiki na yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai a Haiti.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments