Putin : Dogaro Da Kudaden Cikin Gida Zai Iya ‘Yantar Da Kasashe Daga Mulkin Mallaka Na Yamma

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha, ya bayyana kawancen kasashen BRICS wanda ke da kima a fannin siyasar duniya da cewa yana da babbar dama

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha, ya bayyana kawancen kasashen BRICS wanda ke da kima a fannin siyasar duniya da cewa yana da babbar dama ta jawo sabbin mambobi.

Putin, ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na tattalin arzikin kasa da kasa na Saint Petersburg.

Putin ya ce yana maraba da dukkan sabbin mambobi a kungiyar tattalin arziki ta BRICS, yana mai cewa zai yi duk mai yiwuwa don kara sabbin mambobi a kungiyar.

Ya ce cinikayyar da ke tsakanin Rasha da Asiya na kara habaka, inda ya ce cinikin da ake gudanarwa a kasashen yammacin duniya kamar dala da Yuro ya ragu zuwa rabi.

Ya ce a halin yanzu kusan kashi 40 cikin 100 na cinikin waje na Rasha yana kan kudin ruble.

kungioyar BRICS data hada da Brazil, Rasha, Indiya, da China da Afrika ta Kudu ta samu sabbin mambobi a baya bayan nan.

Kasashen Masar, Iran, Habasha, Saudiyya, UAE sun shiga kungiyar a farkon wannan shekara, tare da wasu kasashe 44 kamar Brunei, Cambodia, Indonesia, Laos, Malaysia, Myanmar, Philippines, Singapore, Thailand.

A halin yanzu kasashen BRICS na da yawan jama’ar duniya kusan biliyan 3.5, tare da hadakar tattalin arzikin da ya kai sama da dala tiriliyan 28.5 ko kuma kusan kashi 28 na tattalin arzikin duniya.

Shugaban na Rasha ya sanar da cewa, dogaro da kudaden cikin gida zai iya ‘yantar da wadannan kasashe daga mulkin mallaka na Yamma tare da tabbatar da tsaro na kudi da ingantaccen sha’anin kasuwanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments