Pezeshkian: Iran Za Ta Iya Fuskantar Barazanar Amurka

Majalisar dokokin Iran a hukumance ta fara duba cancantar ministocin da ake shirin sakawa a sabuwar gwamnati, inda shugaba Masoud Pezeshkian ya jaddada muhimmancin wanzar

Majalisar dokokin Iran a hukumance ta fara duba cancantar ministocin da ake shirin sakawa a sabuwar gwamnati, inda shugaba Masoud Pezeshkian ya jaddada muhimmancin wanzar da hadin kai tsakanin bangarorin gwamnati uku domin warware matsalolin kasar.

A wani budadden zama na majalisar a ranar Asabar, Pezeshkian ya gabatar da sunayen ministocinsa 19, ya kuma yi kira da a samar da mafita cikin lumana don tunkarar kalubalen da kasar take da shia  gabata, maimakon daukar wasu matakai da ka iya kawo cikas da tarnaki ga ayyukan ci gaban kasa.

Haka nan kuma ya jaddada cewa gaskiya da rikon amana na gwamnati zai kara dankon dangantaka a tsakanin bangarorin biyu.

“Majalisar ministocin da aka gabatar wa majalisar a yau ita ce ta ta gwamnatin hadin kan kasa; wanda gwamnati ce da take daukar kanta a matsayin gwamnatin dukkanin al’ummar Iran.

Gwamnatin hadin kan kasa ta zama wajibi ta tabbatar da ‘yancin zama dan kasa na dukkan Iraniyawa kuma ta himmatu wajen fifita muradun kasa sama da duk wata maslaha,” in ji Pezeshkian.

Shugaban na Iran ya yi kira da a dauki matakai na hadin gwiwa da hadin kai a tsakanin bangarori uku na gwamnati, domin biyan bukatun al’ummar kasar, shugaban na Iran ya ce: Idan ba a ji muryoyin jama’a cikin lokaci ba, hakan zai haifar da wasu matsaloli a cikin kasa da suka shafi zamantakewar al’umma, inji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments