Pezeshkian: Iran Tana Shirye Ta Kalubalanci Girman Kan Amurka

Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta neman yaƙi, amma za ta tsaya tsayin daka wajen fuskatar girman kan Amurka Shugaban Kasar Iran

Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta neman yaƙi, amma za ta tsaya tsayin daka wajen fuskatar girman kan Amurka

Shugaban Kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Kasarsa ba ta neman yaki, amma ba za ta mika wuya ga barazanar Amurka da matsin lamba ba. Ya jaddada cewa juriyar al’ummar Iran ta canza ra’ayin wasu kasashe game da karfin Iran, kuma gwamnati za ta yi aiki don kawar da cikas ga cinikayya da fitar da kayayyaki da kuma ci gaba da samar da ayyuka ga ‘yan kasa.

Da yake jawabi a ranar Talata yayin bikin ranar fitar da kayayyaki ta kasa karo na 30, Pezeshkian ya bayyana cewa: Amurka ta yi imanin cewa Iran ba za ta iya jure hare-harenta da takunkuminta ba. Duk da haka, ya jaddada cewa: Iran za ta ci gaba da juriyarta kuma ba za ta taba mika wuya ga karfin makiyi da girman kai ba. Ya bayyana godiyarsa ga masu samarwa, masu fitar da kayayyaki da masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziki wadanda kokarinsu a karkashin mawuyacin hali, ya bai wa kasar damar fuskantar matsin lamba da takunkumin da aka sanya mata.

Shugaban Iran ya lura cewa: Juriya da himma al’ummar Iran sun canza fahimtar kasashen makwabta da sauransu game da karfin Iran da matsayinta. Ya jaddada wajibcin samar da yanayin da ake bukata don wadatar kasar da kuma ci gaba da bunkasarta da karfinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted