Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa fararen hula zai iya yin tasiri ga martanin da Tehran za ta mayar a kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
“Idan suka yi bita kan halayensu, suka amince da tsagaita bude wuta tare da daina kashe wadanda ake zalunta da wadanda ba su ji ba ba su gani ba na yankin, hakan na iya yin tasiri ga nau’i martaninmu,” in ji Pezeshkian a zaman majalisar ministoci na wanann Lahadi.
Duk da haka, ya jaddada cewa Iran ba za ta bar hakkinta na daukar matakin da ya dace da duk wani shishigi a kan tsaron kasarta ba.
Shugaban na Iran ya gargadi mahukuntan Isra’ila da cewa za su hadu da martani mai tsanani idan suka yi kuskuren lissafi a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A ranar 26 ga watan Oktoba, jiragen yakin Isra’ila sun yi amfani da sararin samaniyar kasar Iraki a bangaren da Amurka ke kula da shi, wajen harba makamai masu linzami a kan cibiyoyin soji da ke lardunan Tehran, Khuzestan, da Ilam a cikin kasar Iran, lamarin da ya ke a matsayin keta hurumi da kuma dokokin kasar Iraki.
A nasa Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya tabbatar da cewa an kakkabo wani adadi mai yawa na makamai masu linzami, kuma an hana jiragen yakin Isra’ila shiga sararin samaniyar kasar Iran.
Iran dai ta ce ta kuduri aniyar mayar da martani ga matakin da ta bayyana shi da ta’addanci, kuma ba za ta yi watsi da hakkinta a kan hakan ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gargadi Amurka da Isra’ila da cewa ko shakka babu za su yaba wa aya zaki a kan wannan ta’asa da suke aikatawa.