Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adi har zuwa ranar 27 ga Oktoba, 2026, ta dauki matakan biyan bukatun ma’aikata, tana mai gargaɗin cewa za ta iya ɗaukar matakin ƙasa baki ɗaya idan tattaunawar da ake yi ta gaza samar da mafita. Wannan na zuwa ne bayan wani taron tattaunawa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.
Mukaddashin Babban Sakataren NLC, Benson Upah, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis. Ya ce taron da aka gudanar a Ma’aikatar Ƙwadago ya tsaya cak, saboda a cewarsa, wakilan gwamnati sun zo ba tare da cikakken shiri da ikon yanke shawara kan muhimman batutuwan da ake tattaunawa a kansu ba.
Upah ya ce ba a cimma wata yarjejeniya ta zahiri ba, kuma buƙatun da ke gaban ɓangarorin biyu suna nan dai ba a warware su ba. Ya buƙaci rassan NLC na jihohi, da ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da ƙungiyoyin farar hula da ke goyon bayanta su kasance cikin shiri tare da fara shirye-shiryen yiwuwar ɗaukar mataki a faɗin ƙasa. Sai dai ya jaddada cewa ƙungiyar na fatan gwamnati za ta biya buƙatunta ta hanyar tattaunawa.
NLC ta ce za ta ci gaba da bin hanyoyin tattaunawa, amma ba za ta amince da jinkiri marar iyaka ba. Ta kuma bayyana cewa shugabancinta zai yanke shawarar mataki na gaba idan taron ranar Talata bai samar da gagarumin ci gaba ba.