NIREC Ta Bukaci Tinubu Ya Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya

Kungiyar Hadin Kan Addinai ta Nijeriya (NIREC) ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya kawo karshen yawaitar ayyukan ta’addanci da sace-sace da kashe-kashen rayuka

Kungiyar Hadin Kan Addinai ta Nijeriya (NIREC) ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya kawo karshen yawaitar ayyukan ta’addanci da sace-sace da kashe-kashen rayuka a Nijeriya, inda ta ce, lamarin ya wuce abin tsoro.

Majalisar, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), Alhaji Muhammed Sa’ad Abubakar da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), Archbishop Daniel Okoh, sun ce, akwai damuwa matuka game da karuwar rashin tsaro a kasar nan.

NIREC, a cikin wata sanarwa a ranar Talata mai dauke da sa hannun babban sakatarenta, Fr. Farfesa Cornelius Omonokhua, ya ce, kwanan nan ta samu rahoton kashe manoma 13 da aka kashe a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Majalisar ta kuma yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su ci gaba da kula tare da bayar da rahoton duk wani abu da ake zargin ayyukan ta’addanci ne, domin tsaro aiki ne na gama-gari ba na gwamnati kadai ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments