Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ce dai ta fitar da alƙaluma cewa ‘yan Najeriya sun bai wa jami’an gwamnatin ƙasar naira biliyan 721 kwatankwacin dala biliyan 1.26 a matsayin cin hanci a 2023.
Rahoton ya ce ƴan Najeriyar sun bayar da rashawa sau miliyan 87, amma adadin ya yi ƙasa idan aka kwatanta da miliyan 117 da suka bayar a 2019.
Cikin duka ƴan Najeriyan da suka ga aƙalla wani jami’in gwamnati ɗaya cikin wata 12 kafin gudanar da binciken a 2023, kashi 27 sun bai wa jami’in cin-hanci.
Idan aka kwatanta da abin da aka saba gani a baya, hakan na nufin yawan biyan cin-hanci a Najeriya ya ragu kaɗan zuwa kashi 23 tun daga 2019, lokacin da aka samu kashi 29 da suka bayar da cin hanci.
A wuraren da kuma aka tambayi cin-hanci amma mutane suka ƙi bayarwa, an ba da cin-hancin fiye da sau ɗaya cikin haɗuwa uku (kashi 34 cikin 100) a 2023.
Sai dai kuma kashi 70 cikin 100 na mutanen da aka nemi su bayar da cin hancin a 2023 sun ƙi bayarwa sama da sau ɗaya.
Kazalika, binciken ya gano cewa raguwar bayar da cin-hancin ta fi yawa a yankin arewa maso yammacin Najeriya da kashi 76, duk da cewa sauran yankunan sun samu sama da kashi 60 cikin 100.