Mutane 30 Ne Suka Mutu A Harin Da Saudiya Ta Kai Yamen

kasar saudiya ta kai hari yamen ta kashe mutane 30 da jikkata wasu,a yankin taiz

Gidan talabijin din kasar yamen na Al-masira ya nakalto cewa akalla mutane 30 ne suka mutu wasu kuma suka jikkata a cikin sao’I 24 da suka wuce a wani hari da kasar saudiya da kawayenta suka kaddamar a kan fararen hula a lardin Ta’iz da Hajja.

Rahoton da gidan talabijin din almasira ya fitar a safiyar yau jumaa sun nuna cewa hare haren da saudiya da kawayenta suka kai a wurare biyar ma banbanta kan fararen hula ya janwo mutuwar mutane 9 tare da jikkata wasu guda 21, kuma mafi yawancin wadanda suka jikkata mata ne da yara kanana

Haka zalika a wani hari da ta kai a wani gida a yankin al-omari ya kashe mutum daya tare da jikkata wasu guda 8, kuma harin an kai shi ne kai tsaya a kan gidajen fararen hula

Bayanan da ma’aikatar lafiya ta yankin tai’z ta fitar ya nuna cewa matan da suka rasa rayukansu tsakanin yan shekaru 20 zuwa 45 ne, su kuma yaran da suka jikkata kuma tsakanin yan shekara 13 zuwa 10 a harin da suka kai kan iyalai a gidansu da gangan

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted