Kungiyar Musulman Amurka da suka zabi Trump don nuna adawa da matsayar gwamnatin Biden na goyon bayan laifuffukan yakin Isra’ila a Gaza, a yanzu sun fara nuna takaicinsu bayan sanar da sunayen wasu ministocin gwamnatinsa.
Kamfanin dillancin labaran Reutersya bayar da rahoton cewa, da dama daga cikin musulmin kasar Amurka wadanda suka goyi bayan Donald Trump domin nuna adawa da goyon bayan da gwamnatin Biden ta baiwa Isra’ila a kisan kiyashin da take yi a Gaza, sun fara nuna takaici kan kan hakan, musamman ma ganin yadda Trump ya fara nada wasu mukamai na gwamnatinsa, inda yake saka mutane masu tsatsauran ra’ayi wajen kare manufofin Isra’ila.
Trump ya zabi Sanata Marco Rubio na jam’iyyar Republican a jihar Florida a matsayin sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ya shahara da nuna goyon baya ga Isra’ila, wanda a ko shekarar da ta gabata ya fito karara ya bayyana cewa, baya goyon bayan Isra’ila ta tsagaita bude wuta a Gaza, kuma a cewarsa dole ne Isra’ila ta rusa dukkan dakarun Hamas.
A daya bangaren kuma, Trump ya zabi Mike Huckabee, tsohon gwamnan Arkansas kuma dan siyasa mai ra’ayin rikau na goyon bayan Isra’ila wanda ke karfafa Isra’ila kan ci gaba da mamaye yankunan Falastinawa da ke a yammacin gabar kogin Jordan, tare da yin watsi da batun samar da kasashe biyu Falasdinu da Isra’ila kowace mai cin gashin kanta.
Har ila yau, Trump ya zabi Elise Stefanik, wakiliyar majalisar wakilai ta Republican, wadda ta zargi Majalisar Dinkin Duniya da nuna kyamar Yahudawa saboda yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza.
A yayin yakin neman zabe, Trump ya ziyarci garuruwan da ke da yawan mazauna larabawa da musulmi a Amurka, inda ya sheda musu cewa shi shugaban kasa ne na zaman lafiya, kuma zai kawo karshen yake-yake a Gaza da Ukraine.
Reginald Nazarco, babban darektan kungiyar hadin kai da karfafa musulman Amurka ya ce, musulmi masu kada kuri’a sun yi zaton cewa Trump zai zabi mutane masu neman zaman lafiya domin saka sua majalisar ministocinsa, amma sai aka ga akasn hakan, wanda a cewarsa hakan babban abin taiakci ne.