Ministan Harkokin Wajen Kasar  Iran Ya Isa Siriya Bayan Ziyara Mai Muhimmanci A Lebanon

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa birnin Damascus babban birnin kasar Siriya bayan wani ziyara mai muhimmnci da ya kai kasar Lebanon.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa birnin Damascus babban birnin kasar Siriya bayan wani ziyara mai muhimmnci da ya kai kasar Lebanon.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana cewa akwai Shirin tsagaita wuta a Gaza da kuma Lebanon wanda suke shiryawa duk tare da ci gaba da kissan kiyashin da HKI take yi a kasashen biyu Lebanon da Falasdinu.

Labarin ya kara da cewa Aragchi ya fadawa kafafen yada barai haka a lokacinda ya isa birnin Damascus a babban birnin kasar Siriya a safiyar yau Asabar daga birnin Beirut.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin kasar Iran ta bayyana tun farko kan cewa gwamnatin HKI bata san wata hanya ba, sai ta nuna karfi da kuma wuta. Don haka ya sa ke neman kasashen duniya su hada kai don kawo karshen kisan kiyashin da ke faruwa a kasashen Lebanon da Falasdinu da aka mamaye.

Dangane da dangantaka da kasar Siriya kuma Aragchi ya ce, huldar dake tsakanin kasashen biyu tana da fadi, kuma sun hada da tattalin arziki, siyasa, al-adu. Banda haka ana kokarin fadadasu. Sannan muna kokarin kauda sauran matsalolin da kasashen biyu suke fuskanta a sauran fagage.

Aragchi ya je kasar Lebanon da ton 10 na kayakin abinci da magunguna don taimakawa yan gudun hijira da wadanda suka kauracewa gidajensu saboda yakin da kasar ta Fada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments