Ministan harkokin wajen kasar Iran ya ziyarci ofishin kungiyar Hizbullah da ke birnin Tehran fadar mulkin Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyed Abbas Araqchi ya ziyarci ofishin kungiyar Hizbullah ta Lebanon da ke birnin Tehran. Inda ya gana da wakilin kungiyar Sayyid Abdullah Safiyuddeen.
A cikin wannan ganawa da ta gudana a yammacin jiya Talata Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce: Suna jajanta wa kansu da ku dangane da shahadar Sayyed Hassan Nasrallah. Yana mai bayyana rashin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a matsayin babban rashi, to amma hakan ba zai canza al’amura zuwa maslahar yahudawan sahayoniyya ba. A’a zai karawa gwagwarmaya karfi da jajurcewa.
Araqchi ya kara da cewa: Shahadar jagoran kungiyar Hizbullah ba a karon farko ba ne, sai dai kungiyar ta bunkasa ne bayan shahadar Sayyid Abbas al-Musawi, kuma a yau ko shakka babu kungiyar zata iya cimma manufofinta bayan Sayyid Nasrallah.