Ministan Harkokin Wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Matakin tuntubar juna don hada karfi da karfe wajen wanzar da zaman lafiya ya taimaka a fagen guje wa tabarbarewar yankin Gabas ta Tsakiya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Qatar a birnin Tehran cewa: Sun dauki matakin tuntubar juna dangane da fadada gudanar da shawarwari da hada karfi da karfe na yanki da na kasa da kasa domin takaita masifar yaduwar tashe-tashen hankula a yankin.
A rubucinsa a shafinsa na Instagram Araqchi ya bayyana cewa: Sun karbi bakwancin Sheikh Mohammed bin Abdul Rahman Al Thani, fira minista kuma ministan harkokin wajen kasar Qatar da tawagarsa a hedkwatar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, baya ga musayar ra’ayi dangane da ci gaban da ake samu a yankin Gabas ta Tsakiya, sun kuma jaddada bukatar dakatar da laifukan yaki da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza, da kuma hare-haren wuce gona da iri da suke kai wa kan kasar Lebanon, tare da fadada matakin gudanar da tuntubar juna kan batun hadin kai a tsakanin dukkan kasashen yankin da na kasa da kasa domin kaucewa karuwar masifar tashe-tashen hankula da take yaduwa a fadin yankin baki daya.
Araqchin ya kuma kara da cewa: Sun kuma tattauna batun kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da hadin gwiwar su kan batutuwa daban-daban.