MDD, Ta Sanya Isra’ila Cikin Jerin Kasashe Da Kungiyoyin Dake Cin Zarafin Yara

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto da a cikinsa ta sanya sojojin Isra’ila a cikn jerin kasashe da kungiyoyin dake cin zarafin yara.

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto da a cikinsa ta sanya sojojin Isra’ila a cikn jerin kasashe da kungiyoyin dake cin zarafin yara.

A jiya Juma’a ne aka sanar da wakilin Isra’ila da matakin da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yanke.

Bayannin na kunshe ne a rahoton da babban Sakataren MDD, ke mikawa kwamitin sulhu ko wace shekara kan halin da yara ke ciki musamman a yankunan dake fama da fadace-fadacen makamai.

Rahoton ya kunshi irin ta’asar da ta hada da kashe-kashe da raunata yara, cin zarafinsu, sacewa ko hana kai agaji, da kuma kai hari kan makarantu da asibitoci a zirin Gaza.

Isra’ila ta bakin Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu, ta mayar da martani cikin bacin rai, kan rahotonna Majalisar Dinkin Duniya da ya sanya sojojin kasar cikin jerin kasashen da kungiyoyin da suka ci zarafin yara.

Rahoton ya kuma sanya Hamas da kuma ISIS cikin jerin sunayen kungiyoyin da suka ci zarafin yara.

An kusa dai kwashe watanni takwas da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan Gaza, tun bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments