Hukumar bada agaji ta MDD (OCHA) ta bada rahoton cewa sojojin HKI suna amfani da gine ginen makarantu a gaza a matsayin wurin tsare Falasdinawa da suka kama da ransu da kuma maida makarantun a matsayin sansanin sojojinsu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wani rahoton da wani jami’in hukumar ya fadawa tashar talabijin ta Aljazeera ta turanci na cewwa akalla kashi 68% na makarantun Gaza sun rushe saboda hare haren jiragen yaki da kuma makaman HKI a kansu.
Rahoton na OCHA ya kara da cewa hotunan tauraron dan’adam sun nuna cewa sojojin HKI sun maida gine ginen makarantu da dama a gaza a matsayin sansanin sojojinsu da kuma azabatar da Falasdinawa da suka kama da ransu.
Rahoton ya kara da cewa kashi 38% na makarantu a Gaza wadanda yawansu ya kai 212 sun lalace kuma suna bukatar a sake gina su saboda makaman sojojin HKI da suka fada kansu.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ce sojojin HKI suka fara ruwan boma bomai a kan gaza, da suna shafe kungiyar Hamas da kuma kwato yahudawan da suke tsare a hannun yayan wannan kungiyar.