A wani bayani da mayakan kungiyar Hizbullah su ka fitar sun bayyana girman barnar da su ka yi wa sojojin mamaya tun daga lokacin da suke kokarin yin kuste cikin Lebanon.
Bayanin ya kunshi cewa ya zuwa yanzu sun kashe sojojin mamaya 95, da kuma tarwatsa tankokin yaki 42.
Bayanin da aka fitar da shi a jiya Alhamis ya kuma ce, ana yin bata-kashi ne da sojojin mamaya da suke son yin kutse cikin Lebanon ta hanyoyi biyar da suke kan iyaka,sannan kuma a lokaci daya ana cigaba da harba makamai masu linzami cikin yankuna mabanbanta da suke karkashin mamaya.
Baya ga sojojin da aka kashe, an kuma jikkata wasu da adadinsu ya kai 900, da kuma lalata tankokin yaki samfurin “Mirkava” da su ka kai 42 da kuma motocin yin rusau “ Buldoza” guda biyu. Haka nan kuma ‘yan gwgawarmayar sun harbo jiragen sama marasa matuki samfurin ‘ Hermes 450” guda uku, sai kuma samrufin “Hermes 900” guda biyu.
Kokarin yin kutsen da sojojin mamayar na HKI suke yi ta kasa zuwa cikin Lebanon, bai hana ‘yan gwagwarmayar cigaba da kai hare-hare ta makamai masu linzami ba a cikin sansanonin kusa da kan iyaka da kuma wadanda suke nesa har zuwa birnin Tel Aviv da nesa da shi.