Mataimakin Shugaban Kasar Malawi Ya Rasu Sanadiyyar Hatsarin Jirgin Sama

Mataimakin shugaban kasar Malawi da mutane 9 da suke tare da shi sun rasa rayukansu sanadiyyar hatsarin wani karamin jirgin saman da ke dauke da

Mataimakin shugaban kasar Malawi da mutane 9 da suke tare da shi sun rasa rayukansu sanadiyyar hatsarin wani karamin jirgin saman da ke dauke da su a tsakanin tsaunuka a ranar Litinin da ta gabata.

Shafin yanar gizo na labarai Africanews ya bayyana cewa shugaban kasar Malawi  Lazarus Chakwera ne da kansa ya bayyana haka a jiya talata a wani jawabinda yayiwa mutanen kasar, ya kuma kara da cewa masu kula da zirga zirgan jiragen sama a kasar sun kasa magana da matukin jirgin bayan da suka bashi umurni ya dawo Lilongwe babban birnin kasar saboda bacin yanayi.

Shugaban ya kara da cewa daga baya jami’an agajin gaggawa sun sami burbucin jirgin da kuma gawakin mutane 10 daga ciki har da na mataimakin shugaban kasar Saulos Chilima a kan tsaunukan kasar.

Chilima dan shekara 51 a duniya yana mataimakin shugaban kasa karo na biyu ne, kuma ana saran da ya rayu zai shiga takarar shugabancin kasar mai zuwa.

Shugaba kasa ta Malawi Chakwera ya mika ta’aziyyarsa ga mutanen kasar Malawi musamman kuma danginsa dangane da rashin mataimakin shugaban kasa. A shekara ta 2022 ne dai, aka kama Chilima tare da tuhumar almundaha, amma an yi watsi da karar a cikin watan da ya gabata. Sannan ya musanta cewa ya aikata wani laifi.

A halin yanzu dai sojojin kasar suna kokarin dawo da gawakinsu zuwa babban birnin kasar, kafin a sa lokacin jana’izarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments