Masanin Harkokin Siyasa Ya Ce  Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Boye Hasarorin Da Ake Janyo Mata A Yaki

Daraktan Cibiyar Nazarin Siyasa da Zamantakewa ta Larabawa ya ce: Duk wata hasara da gwamnatin yahudawa ke boye wa… Tauraron Dan Adam yana fallasa abin

Daraktan Cibiyar Nazarin Siyasa da Zamantakewa ta Larabawa ya ce: Duk wata hasara da gwamnatin yahudawa ke boye wa… Tauraron Dan Adam yana fallasa abin da ke boye!

Riyadh Sidawi, Daraktan Cibiyar Nazarin Siyasa da Zamantakewa ta Larabawa daga Geneva, ya bayyana cewa: Hasarar da yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya suke boye wa bayan harin “Alkawarin Al-Sadiq na biyu” na jarumtaka, babbar hasara ce, kuma abin da yahudawa suke boye wa ya wuce girman yadda ake tsammani.

Sidawi ya yi nuni da cewa: Wanda ake kira Benjamin Netanyahu ya kasance mai alfahari kamar Talo-talo, kuma ya yi imanin cewa ta hanyar kashe shahidi Sayyid Hassan Nasrallah jagoran gwagwarmaya ya kawo karshen gwagwarmayar kungiyar Hizbullah, don haka ‘yan gwagwarmaya suka koya masa darasi ta bangarorin da dama ta hanyar mayar da martanin Iran da aka yi amfani da makamai masu linzami wadanda suke dauke da ci gaba mai muhimmanci, a cikin ‘yan mintoci kaɗan kawai wadannan makamai masu linzami suna tafiya kilomita 1,400, kuma suna da matukar wuya a harbo su ko hana kutsensu. Seddawi ya kara da cewa: ‘Yan jaridun kasashen waje ne suka tona tare da fallasa abubuwan da ake boye wa, sannan suka nuna hotunan tauraron dan Adam na filayen jiragen sama na soja da makaman suka barna ta masu yawa, da ruguza gine-gine, da kuma tarwatsa jiragin sama F-35 da F-22 masu matukar ci gaba, don haka wadannan hare-hare na Iran sun kasance masu zafi da radadi kan haramtacciyar kiasar Isra’ila, kuma hatta jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar Isra’ila da kanta, ta yi furuci da zafin wannan martani, tana cewa: Na’urorin tsaronsu na sama sun samu matsalar da ba zasu iya tunkarar hare-haren ba a halin yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments