Londan: Mai Yuwa Julian Assange Ya Sasanta Da Amurka A Mako Mai Zuwa Don Samun Damar Sakinsa

Mutumin da ya samar da shafin yanar gizo ta Wiki Leaks kuma dan jarida wato Julian Assange ya shiga cikin tattaunawa da gwamnatin kasar Amurka

Mutumin da ya samar da shafin yanar gizo ta Wiki Leaks kuma dan jarida wato Julian Assange ya shiga cikin tattaunawa da gwamnatin kasar Amurka wanda mai yuwa hakan ya bashi damar samun yenci da kuma sakinsa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tun shekara ta 2019 ne ake tsare da shi a gidan yarin Belmarsh na birnin Londan, bayan da gwamnatin kasar Burtania ta sami izinin fito da shi daga ofishin jakadancin kasar Ecuado a birnin Lodan inda yake samun mafaka tun shekara ta 2012.

Gwamnatin Amurka na zargin Assange ta aikin liken asiri bayan da ya watsa takardun sirrin kasar na aikata kisan kare dangi a yankin da ta yi a kasashen Iraki da Afganistan.

Har’ila yau tana zarginsa da watsa dakardun sirrin gwamnatin Amurka wadanda yawansu ya kai shafi 700,000. Kuma sun kunshi ayyukan soje na Amurka tun shekara ta 2010.

Tun lokacinda ya wallafa bayanan ne gwamnatin Amurka take neman a mika mata shi don ya gurfana a gaban kuliya a Amurka, inda masana suna ganin za’a daure shi har na tsawon shekari 175.

Amma a halin yanzu idan al-amarin ya tafi kamar yadda aka tsara Assange zai amince da laifi guda a gaban kotu sannan a yanke masa huklunci wanda zai yi dai dai da zaman kason da yayi a Belmarsh. Sannan sai a sake shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments