Likitoci Sun Bincika Gawar Sayyid Nasrallahi A Asibiti Domin Gano Musabbabin Shahadarsa

An kai gawar shahid Sayyed Hasan Nasrallah zuwa asibiti domin bincike dalilin mutuwarsa Majiyoyin yada labaran kasar Lebanon sun sanar da cewa: An dauki gawar

An kai gawar shahid Sayyed Hasan Nasrallah zuwa asibiti domin bincike dalilin mutuwarsa

Majiyoyin yada labaran kasar Lebanon sun sanar da cewa: An dauki gawar marigayi shahidi babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrallah zuwa asibiti a birnin Beirut domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar.

Majiyoyi biyu sun shaidawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa: Bayan gudanar da cikakken binciken gawar Sayyed Hassan  Nasrallah babu wani rauni da ya samu kai tsaye daga fashewar bama-baman, kuma hujja mai karfi na dalilin mutuwarsa bisa ga alamu firgita ce daga tsananin karfin karar fashe-fashen bama-baman.

Sannan binciken farko da aka yi wa gawar shahidi Sayyed Hassan Nasrallah ya nuna cewa ba a yi masa lahani kai tsaye ba a wani bangare na jikinsa. Rahotonni sun bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai harin kan wurin da ta tabbatar babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah yana wurin ne da bama-bamai masu nauyin ton 85, lamarin da ya saba wa dukkanin ka’idojin kasa da kasa har da Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments