Lavrov: Washington tana karfafa ‘Isra’ila’ domin ta mamaye kasar Lebanon

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana a wannan Juma’a cewa, Amurka tana baiwa “Isra’ila” kwarin gwiwar fadada kutsenta a cikin kasar Lebanon,

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana a wannan Juma’a cewa, Amurka tana baiwa “Isra’ila” kwarin gwiwar fadada kutsenta a cikin kasar Lebanon, inda ta kasa yin ko da Allah wadai ne da yunkurin Isra’ila na mamaye kudancin Lebanon.

A cikin wata sanarwa da babban jami’in diflomasiyyar na Rasha ya fitar ya ce, tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da shirin mamaya a  kasar Lebanon a daren ranar 1 ga watan Oktoba, babu wata kalma guda daya ta yin Allah wadai da gwamnatin Amurka ta furta kan wannan ta’addancin da ake yi wa wata kasa mai cin gashin kanta. Ya kara da cewa “Ta haka, a zahiri Washington tana karfafa gwiwar Isra’ila domin  ci gaba da fadada yakin da take yi a gabas ta tsakiya.

A cewar Lavrov, wanda ya yi tsokaci kan abubuwan da ke da ban tausayi da suka shafi yakin, wanda Tarayyar Rasha ta kira rikici tsakanin Larabawa da ayyukan mamaya na Isra’ila, ya ce dole a kawo karshen wadannan ayyuka na Isra’ila domin samu zaman lafiya  ayankin.

Lavrov ya kuma yi Allah wadai da yadda haramtacciyar kasar Isra’ila ke aiwatar da kisan gilla a yankin gabas ta tsakiya da kuma wanda ta yi a  birnin Tehran, ya kuma yi Allah wadai da ayyukan  “Isra’ila” na keta hurumin kasar Labanon a kan iyakar kudancin kasar, wadda kasa mai cikakken ‘yanci kuma mamba a majalisar dinkin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments