Kwamitin Sulhu ya bukaci a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana bacin ransa kan rashin samun ci gaba a tattaunawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da nufin kawo karshen

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana bacin ransa kan rashin samun ci gaba a tattaunawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da nufin kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ta kwashe watanni tana yi a kan Falasdinawa a zirin Gaza da aka yiwa kawanya.

Kwamitin mai wakilai 15 ya gudanar da taron gaggawa karo na biyu a kan Gaza cikin kasa da mako guda a ranar Laraba, inda ake ci gaba da yin kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a yankin Falasdinu da Isra’ila ta yi kawanya, yayin da mambobin kwamitin  suka tattauna kan halin da ake ciki a bangaren ayyukan  jin kai da kuma a halin da ake ciki a yammacin kogin Jordan.

Mambobin majalisar sun bayyana bacin ransu kan kin amincewar da Isra’ila ta yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka zayyana a kuduri mai lamba 2735, wanda ya bukaci a saki fursunonin da kuma janyewar Isra’ila daga Gaza.

Jakadan Slovenia Samuel Žbogar, wanda tawagarsa ke rike da shugabancin kwamitin a wannan watan, ya ce “kasashen duniya suna bakin ciki matuka kan cewa har yanzu wannan yaki bai tsaya ba.

Žbogar ya tunatar da mambobin kasashe 15 cewa aikinsu ne su samar da zaman lafiya.

Rosemary Anne DiCarlo, mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin siyasa da samar da zaman lafiya, ta jaddada bukatar tsagaita bude wuta nan take a Gaza, da kuma gaggauta kai kayan agaji ga yankin zirin gaza da ke Falasdinu da Isra’ila ta yi wa kawanya.

DiCarlo ta yaba da ci gaba da kokarin da kasashe masu shiga tsakani suke yi na ganin an tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta ce tarurrukan baya-bayan nan a Doha da Alkahira sun yi kokarin dinke barakar da ke akwai, amma har yanzu akwai manyan bambance-bambance tsakanin manufar da ake son a cimmawa da kuma matsayar bangarorin biyu.

Ta kara da cewa, halin da ake ciki a kasa yana da muni da ban takaici, inda sojojin Isra’ila ke ci gaba da gudanar da ayyukansu a duk fadin Gaza, kuma adadin wadanda suka mutu ya karu matuka, tana mai jaddada cewa dole ne Isra’ila ta yi aiki bisa dokokin kasa da kasa na kare fararen hula da tabbatar da tsaronsu da kare lafiyarsu.

Riyad Mansour, jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya, ya jaddada wajabcin tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza, ya kuma ce Isra’ila na amfani da hanyoyi daban-daban na yaudara da kuma wawantar da al’ummomin duniya domin cimma manufofinta na mulkin mallaka a yankin yammacin kogin Jordan.

“Isra’ila ta kaddamar da cikakken yaki akan al’ummar Palasdinu, Isra’ila na neman hanyar magance rikicin ta hanyar share wata al’umma daga doron kasa baki daya, babu musun wadannan hujjoji, tun daga kisan kare dangi zuwa nuna wariya, Isra’ila tana nunawa duniya  cewaa shirye take ta yi aiki da dokokin kasa da kasa da kuma dakatar da yaki, sannan kuma a daya bangaren tana yin watsi da dukkanin dokoki na duniya tare da yin gaban kanta wajen aiwatar da abin da ta ga dama a kan idon al’ummomin duniya, ba tare da wani ya isa ya taka mata burki ko kuma yace mata uffan ba, saboda cikakken goyon baya da take das hi kai tsaye daga manyan kasashen turai.

“Muna bukatar tsagaita bude wuta, a tsagaita bude wuta a yanzu, kowa yanafadin haka ba Falasdinawa kawai ba, har ma miliyoyin yahudawan Isra’ilawa da ke zanga-zanga a kan tituna, wadanda suka damu da wadanda aka yi garkuwa da su. Kuma suna kiran shugabanninsu wadanda basa saurarensu da cewa, ” A dakatar da bude wuta a yanzu.

Amar Bendjama, jakadan Aljeriya kuma wakilin dindindin na kasa a Majalisar Dinkin Duniya, ya zargi kwamitin sulhun da gaza aiwatar da kudurorinsa na dakatar da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, ya kuma ce, “Muna fuskantar jarrabawa dangane da yadda muke bin dokokin kasa da kasa da kuma wannan tsari na bangarori daban-daban.”

“Muna a wannan wuri a yau saboda diflomasiyya, amma kuma mun gaza, ta yaya za mu iya dakatar da wahalhalun al’ummomin duniya ,” in ji shi, ya kara da cewa bai kamata diflomasiyya ta kasance da harshen damo ba, a lokacin da ake Magana kan batun mawuyacin hali da wahalhalu na fararen hula  da Isra’ila ta jefa su a Gaza ba, yayin da inda hakan an faruwa ne a wani na daban a duniya, da tuni an ji muryoyi suna tashi sama ana ta tofin Allah tsine da Allawadai, wata kila har ma da daukar matakai na soji da sunan kare rayukan fararen hula, wanda a cewarsa hakan ya kara fito da munafunci da salon a siyasar harshen damo na kasashe masu karfin fada a ji a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments