Kungiyar kare farar hula ta Falasdinu ta zargi sojojin da ” kashe-kashe masu yawa”

Kungiyar kare farar hula ta Falasdinu ta zargi sojojin da ” kashe-kashe masu yawa” a yayin farmakin da ya kashe ma’aikatan jinya 15 a cikin

Kungiyar kare farar hula ta Falasdinu ta zargi sojojin da ” kashe-kashe masu yawa” a yayin farmakin da ya kashe ma’aikatan jinya 15 a cikin watan Maris a zirin Gaza, wanda ya saba wa sakamakon wani rahoton bincike na cikin gida da sojojin Isra’ila suka fitar.

Wani jami’in tsaron farar hula a Gaza Mohammed al-Moughair ya shaidawa AFP cewa “Bidiyon da daya daga cikin ma’aikatan jinya ya dauka ya tabbatar da cewa rahoton da sojojin Isra’ila suka fitar akwai karairayi a ciki saboda ta aiwatar da hukuncin kisa.

Al-Moughair ya kuma zargi Isra’ila da neman kaucewa abinda ya wajaba kanta a karkashin dokokin kasa da kasa.

Tunda farko dama Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta yi watsi da rahoton da sojin Isra’ila suka fitar kan kisan da aka yi wa sama da jami’an agajin gaggawa na Gaza a watan da ya gabata, wanda gwamnatin kasar ta ce an kashe ne ta bisa kuskure.

Kungiyar ta yi fatali da rahoton na Isra’ila da cewa ba shi da inganci kuma ba za a amince da shi ba, tana mai jaddada cewa yana cike da karairayi.

A wani rahoto da suka fitar ka abinda ya faru sojojin Isra’ila sun yi ikirarin cewa, an samu ” kura-kurai da yawa” a kisan da akayi wa jami’an agajin a Gaza, suna masu cewa za a kori wani kwamandan sojoji.

“Binciken ya nuna cewa an samu wasu matsaloli na rashin da’a na kwararru, da rashin bin umarni, da kuma gaza yin cikakken bayani kan lamarin,” in ji rundunar.

A ranar 23 ga Maris, ne aka harbe wasu ma’aikatan agaji na Falasdinawa 15 da masu aikin ceto a kusa da Rafah da ke kudancin Gaza.

Kisan da akayi wa jami’an agajin gaggawa na falasdinu ya fuskanci tofin Allah-tsine daga kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments