Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta watsa wani mummunan hari da ta kashe sojojin yahudawan sahayoniyya 10
Kafafen yada labaran soji da suke da alaka da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, sun wallafa faifan bidiyon Dakarun Hizbullah suka tarwatsa wani taron gungun sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da makamai masu linzami a tsakanin garuruwan Kafr Kila da Deir Mimas da ke kudancin Lebanon a yammacin jiya Lahadi.
Faifan bidiyon ya nuna yadda sojojin mamayar suka zube kasa, wadanda adadinsu ya haura 10, a lokacin da suka tunkari wani gini domin kai harin wuce gona da iri, kuma an kai musu harin ne da makami mai linzami kirar Kornet lamarin da ya yi sanadin afkawarsu cikin ginin tare da tashin gobara.
Bayan kai harin, sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun harba bama-bamai da ya janyo tashin hayaki, inda suka yi saurin kwashe wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.