Kungiyar Hizbullah Ta Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar da kai jerin  hare-hare karkashin taken “Khaybar” kan haramtacciyar  kasar Isra’ila Majiyoyin watsa labaran yahudawan sahayoniyya sun bayyana

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar da kai jerin  hare-hare karkashin taken “Khaybar” kan haramtacciyar  kasar Isra’ila

Majiyoyin watsa labaran yahudawan sahayoniyya sun bayyana cewa: Hare-haren sun yi sanadiyyar jikkatan yahudawa da barna ta kayayyaki da kuma tashin gobara a yau Talata, kuma hare-haren da aka kai daga kasar Lebanon da makamai masu linzami sun fado ne kai tsaye a birnin Tel-Aviv babu wani na’urar kakkabo makamai da ya yi nasarar kakkabo su.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar da cewa: Mayakanta sun harba makamai masu linzami samfurin Fadi nau’in 4, kan sansanin Galilot na sashin leken asirin soja na bataliya ta 8200 da kuma kan hedkwatar Hukumar leken asirin yahudawan sahayoniyya ta Mossad, wanda ke wajen birnin Tel Aviv.

Kungiyar ta Hizbullah ta kuma kai hari da makami mai linzami kirar Khaybar kan birnin Tel Aviv kuma harin ya zo ne a cikin tsarin ayyukan Khaybar da kuma mayar da martani ga hari kan fararen hula da kisan kiyashi da makiya yahudawan sahayoniyya suka yi kan al’ummar Lebanon.

Kafofin yada labaran yahudawan sun yi ikrari da cewa: Yahudawan sahayoniyya guda biyu sun jikkata wasu kuma sun shiga cikin halin firgici, baya ga barna da tashin gobara da harin ya janyo a birnin na Tel Aviv fadar mulkin yahudawan sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments