Kungiyar Hamas Ta Bukaci Goyon Baya Daga Sauran Falasdinawa Na Gabar Yammacin Kogin Jordan

Kungiyar Hamas ta yi kira ga jami’o’in Yammacin Kogin Jordan da su shirya zanga-zangar nuna goyon baya ga Gaza da kuma kin amincewa da kisan

Kungiyar Hamas ta yi kira ga jami’o’in Yammacin Kogin Jordan da su shirya zanga-zangar nuna goyon baya ga Gaza da kuma kin amincewa da kisan kare dangi

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta yi kira ga jami’o’in Yammacin Kogin Jordan da su tashi tsaye wajen gudanar da gangami da zanga-zanga a ranar Talata, domin nuna goyon baya ga Gaza, da tsayin dakanta, da kuma kawo karshen kisan kiyashi.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, shugaban kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bukaci ‘yan Falasdinu gami da daliban jami’o’in Falasdinu masu ‘yanci a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suke mamaye da su da su tashi tsaye tare da gudanar da zanga-zangar bacin rai da aka shirya za a fara a yau Talata, domin nuna goyon baya ga zirin Gaza da kuma yin watsi da yakin da ake yi na kawar da al’ummart yankin.

Jagora Shadid ya jaddada cewa, dole ne kungiyar dalibai a yammacin gabar kogin Jordan ta taka rawa wajen dakatar da kisan kiyashi da kuma daukar matakan gaggawa ga Gaza a dukkanin fagagen jama’a da jami’o’i, yayin da ake ci gaba da yakin kisan kiyashi da kuma fatattakar da ‘yan gwagwarmaya suke ci gaba da gwabza fada a fagen yakin ambaliyar al-Aqsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments