Kungiyar BRICK Ta Rattaba Hannu A Kan Yarjeniyar Raya Ayyukan Noma A Duniya

A ranar 17 ga watan Afrilun da muke ciki ne wakilai ko ministocin noma na kasashen kungiyar BRICS suka taro a Brazilian a kasar Brazil

A ranar 17 ga watan Afrilun da muke ciki ne wakilai ko ministocin noma na kasashen kungiyar BRICS suka taro a Brazilian a kasar Brazil inda suka rantaba hannu kan shelanta shirin namusamman na bunkasa ayukan noma da kuma harkokin samar da abinci da kuma wadatar da shi ga kasashen duniya farko ga kasashen kungiyar.

Shirin dai ya hada da na shekara ta 2021-2024 da kuma na 2025-2028, wadanda kungiyar zata aiwatar da su tare.

Shirin ya hada da bunkasa ayyukan noma da samar da wuraren ajiye kayakin noma da kuma taimakawa kananan ayyukan noma a kasashen kungiyar saboda smaar da manoma wadanda zasu yi noma mai yawa nan gaba. Sannan rage abubuwan da ke hana ayyukan noma ci gaba a cikin kasashen kungiyar .

Kasashen kungiyar BRICS dai suna da kasha 54.5 % na yawan mutane a duniya, sannan suna noman 1/3 na filayen noma a duniya, wanda zai bada damar aiwatar da dukkan wadannan ayyuka da sauki da kuma sauri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments