Kisan Nasrallah : Zaman Makokin Kwanaki Uku A Kasashen, Lebanon, Iraki Da Siriya

Kasashen Lebanon, Iraki, da kuma Siriya daya bayan daya duk sun ayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa, boyi bayan shahadar shugaban kungiyar Hezbollah

Kasashen Lebanon, Iraki, da kuma Siriya daya bayan daya duk sun ayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa, boyi bayan shahadar shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah.

Kasar Lebanon ta sanar da zaman makoki na kwanaki uku bayan rasuwar Hassan Nasrallah.

Firayim Ministan kasar Najib Mikati ya ce za a fara zaman makoki a hukumance a ranar Litinin, 30 ga watan Satumba, tare da rage tutoci a kan gine-gine, a cewar wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa, za a kuma rufe ofisoshin gwamnati a ranar jana’izar Nasrallah, ko da yake har yanzu kungiyar Hizbullah ba ta bayyana ranar ba.

Syria ma ta yi Allah wadai da “kisan”, na Nasrallah, inda ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa.

Syria, wacce ke kawance da kungiyar Hizbullah ta Lebanon, ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shugaban na Hizbullah, tare da yin Allah wadai da “mummunan zaluncin” in ji ma’aikatar harkokin wajen Syria a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa “Al’ummar Siriya ba za su taba mantawa da goyon bayan da suke bayarwa ba.’’, in ji kamfanin dilancin labaren Sana.

A kasar Iraki, ma an nuna fushi, kan kisan na Hizbollah, inda ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku bayan rasuwar Hassan Nasrallah

A birnin Basra da ke kudancin kasar Iraki da kuma birnin Bagadaza daruruwan mutane ne suka fito kan tituna domin nuna bacin ransu kan harin da Isra’ila ta kai wanda ya kai ga shahadar Hassan Nasrallah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments