Kashi 62% na yahudawan Isra’ila ba za su zabi Netanyahu a zabe mai zuwa ba

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da tashar talabijin ta 12 ta Isra’ila ta gudanar, ta nuna gagarumin sauyi a fagen siyasar Isra’ila, inda akasarin yahudawa ke

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da tashar talabijin ta 12 ta Isra’ila ta gudanar, ta nuna gagarumin sauyi a fagen siyasar Isra’ila, inda akasarin yahudawa ke nuni da cewa ba za su zabi firaminista Benjamin Netanyahu ba ko kuma jam’iyyar da ke mara masa baya a zabe mai zuwa.

Binciken wanda aka bayar da sakamakonsa a ranar Juma’a ya nuna cewa kashi 62% na wadanda aka ji ra’ayinsu ba sa son kada kuri’unsu ga jam’iyyar da ke goyon bayan Netanyahu. Sabanin haka, kashi 19% ne kawai suka bayyana goyon bayan jam’iyyun da ke goyon bayan Netanyahu, yayin da wasu 19% na wadanda suka amsa ba su yanke shawara ba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Netanyahu ke ci gaba da marawa yakin Gaza baya, wanda ya janyowa Isra’ila matsaloli da dama musamman na kudi. Wani muhimmin batu kuma, shi ne yadda Isra’ila ke ci gaba da kin amincewa da tsagaita bude wuta a zirin Gaza.

Netanyahu ya kuma fuskanci koma baya ga shirinsa na sake fasalin shari’a, wanda ke neman takaita karfin bangaren shari’a. Wannan shiri dai ya fuskanci turjiya mai karfi daga bangarori daban-daban na yahudawa, lamarin da ya kara ruruta wutar zanga-zangar adawa da shugabancinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments