Kasashen Iran, Turkiyya Da Rasha Sun Tattauna Batun Kasar Siriya A Gefen Taron Babban Zauren MDD A Birnin New York

Ministocin harkokin waje na kasashen Iran, Turjiyya da kuma Rasha sun hadu a gefen taron babban zauren MDD inda suka  tattauna dangane da kasar Siriya.

Ministocin harkokin waje na kasashen Iran, Turjiyya da kuma Rasha sun hadu a gefen taron babban zauren MDD inda suka  tattauna dangane da kasar Siriya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyanacewa cewa kasashen uku da farko sun yi allawadai da hare haren jiragen yakin HKI a kan birnin Beirut na kasar Lebanon wanda ya kai ga shahadar shugaba kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah.

Labarin ya kara da cewa ministocin harkokin wajen kasashen Iran, Abbas Araghchi, na Rasha, Sergey Lavrov, da kuma na Turkiyya Hakan Fidan sun yi tattaunawar ne a jiya Asabar a gefen taron babban zauren MDD karo na 79Th  da ke gudana a birnin New York a halin yanzu.

Babban maganar da bangarorin uku suka tattauna a kansa shi ne batun kasar Siriya da kuma yadda yake-yake a kasar Falasdinu da Lebanon suka kawo cikas a cikin al-amarin warware rikicin kasar ta Siriya karkashin tattaunawa ta Astana.

Sun kuma bukaci a farfado da tattaunawar Astana don warware matsalolin da kasar Siriya take fama da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments