Kasashen Iran Da Rasha Suna Bunkasa Alakar Da Take Tsakaninsu

Wanda yake rike da mukamin shugabancin kasar Iran, da kuma shugaban kasar Rasha, sun gana da juna a yayin taron kungiyar Shanghai a kasar Kazakistan.

Wanda yake rike da mukamin shugabancin kasar Iran, da kuma shugaban kasar Rasha, sun gana da juna a yayin taron kungiyar Shanghai a kasar Kazakistan.

Mai rike da mukamin shugaban kasar ta Iran Muhammad Mukhbir ya isa birnin Astana na kasar Kazakhstan ne a jiya Laraba, domin halartar taron kungiyar Shangahi wanda shi ne karo na 24.

Muhammad Mukhbar ya yaba da rawar da kungiyar ta Shanghai take takawa da kuma gudanar da ayyuka tare a tsakanin kasashen da suke mambobi.

A gefen wannan taron, an yi ganawa a tsakanin shugabannin na Iran da kuma Rasha Vladmir Putin.
A yau 4 ga watan Yuli ne dai aka bude taron kungiyar da shi ne karo na 24 wanda kuma zai cigaba har zuwa gobe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments