Kasashen duniya sun yi maraba da fitar da sammacin kama fira ministan gwamnatin Isra’ila da tsohon ministan yakinsa
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar da sammacin kamo fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan yakinsa Yoav Gallant.
A cikin wata sanarwa da Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta fitar a jiya Alhamis ta jaddada cewa: Ana tuhumar Netanyahu da Gallant ne da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’ Adama.
Sanarwar ta yi nuni da cewa: Akwai dalilai masu tarin yawa da ma’ana da suka tabbatar da cewa: Netanyahu da Gallant sun jagoranci kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan fararen hulan Falasdinawa a Zirin Gaza.
Kotun tana mai fayyace cewa: Laifuffukan da ake zargin Netanyahu da Gallant sun hada da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki.
Kamar yadda kotun hukunta manyan laifukan ta kasa da kasa ta tabbatar da cewa: Amincewar haramtacciyar kasar Isra’ila da hurumin kotun bai zama dole wajen halaccin matakanta ba.