Jami’in kasar Yemen ya jaddada cewa: Kwanaki masu zuwa za su aiwatar da abubuwan mamaki da za su ba abokan gabanmu mamaki!
Daraktan sashin yada labarai na fadar shugaban kasar Yemen Zaid Al-Gharsi ya jaddada samun gagarumin ci gaba a karfin sojojin kasar Yemen musamman a fannin fasaha da makamai. Ya yi nuni da cewa, kasar Yemen na gab da samar da sabbin makamai da za su bai wa kowa mamaki.
A cikin wata hira da tashar talabijin ta Al-Alam, Zaid Al-Gharsi ya yi magana game da irin goyon bayan da kasar Yamen ke ba wa yankin Zirin Gaza, inda ya yi nuni da mahimmancin hare-haren soji kai tsaye kan makiya ‘yan sahayoniyya tare da jaddada fifikon karfin kasar Yemen idan aka kwatanta da na ‘yan sahayoniyya da Amurkawa.
Al-Gharsi ya bayyana cewa, yakin da ake yi a halin yanzu yana da manyan fasahohi, saboda makiya ‘yan sahayoniyya sun mallaki fasahar soji na zamani da kuma dogaro da goyon bayan Amurka.