Iran Ta Ce Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita

Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar

Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma wasu mutane da dama masu fafutuka a shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lumana takunkumi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya bayyana manufar takunkuman da Amurka ta kakabawa al’ummar Iran da cewa; A fili take nuna kyama ga masu yanke shawaran Amurka kan al’ummar Iran da kuma nuna rashin mutunta doka da hakkin dan Adam ne.

Ya kara da cewa: Dogaro da tsarin gwamnatocin Amurka da suka shude kan takunkumin tattalin arziki a kan kasashe masu tasowa, a matsayin makamin tsoratarwa da matsin lamba na siyasa, wani lamari ne da ya saba wa muhimman ka’idojin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma dokokin kasa da kasa, kuma yana yin zagon kasa ga ginshikin doka da ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, kuma yana haifar da keta hakkin bil’adama na asali na al’ummomin da takunkumin ya shafa, musamman ‘yancin ci gaba. Wannan hali sau da yawa yana zama laifi ga ɗan adam.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments