Search
Close this search box.

Kasar Cuba Ta Soki  Rahoton Amurka Na Shekare-Shekara Akan Hakkin Bil’adama

Ministan harkokin wajen kasar Cuba Bruno Rodríguez Parrilla  ya yi watsi da rahoton da Amurka ta fitar dangane da yanayin hakkin bil’adama a cikin kasar

Ministan harkokin wajen kasar Cuba Bruno Rodríguez Parrilla  ya yi watsi da rahoton da Amurka ta fitar dangane da yanayin hakkin bil’adama a cikin kasar Cuba a 2023.

Ministan harkokin wajen kasar ta Cuba ya wallafa sako a shafinsa na X yana mai cewa: “ Ba batun kare hakkin bil’adama ne ya damu sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blenkin ba,maimakon haka ne Amurkan tana kara matsin lamba ne akan al’ummar Falasdinu da takura musu da hana su shakar lumfashi da kuma yi musu kisan kiyashi.

Ministan harkokin wajen kasar ta Cuba ya kuma kara da cewa; Abinda ya damu Amurka wanda yake gabanta shi ne kare manufofin manyan kamfanonin da suke kera makamai da kuma shimfida ikonta a duniya.

A cikin rahoton shekara-shekara da Amurka ta fitar ta zargi kasashen da take gaba da su da take hakkokin dan’adam da suka hada Cuba, Rasha, Blarus, Ncragua, da Venezuela. Sai kuma kasashen  China, Uganad, Iran da Afghanistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments