Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Jaddada Muhimmancin Zaben Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana fitowar al’ummar Iran a zaben shugaban kasa da za a gudanar a kasar a matsayin ƙarfafa karfin Jamhuriyar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana fitowar al’ummar Iran a zaben shugaban kasa da za a gudanar a kasar a matsayin ƙarfafa karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a duniya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naser Kan’ani ya bayyana cewa: Fitowar al’ummar Iran kwansu da kwarkwatarsu a lokacinh zaben shugaban kasa lamari ne da zai karawa kasar Iran karfi da ikon fada a ji a matakin yanki da na kasa da kasa.

A rubutun da ya yi a shafinsa na sadarwa Nasir Kan’ani ya jaddada cewa: Zabe a Iran wata alama ce ta dimokaradiyyar addini, kuma yadda al’ummar Iran ke yawan shiga zabukan ya sanya su taka rawar gani mai inganci da azama wajen tafiyar da kasar, da kuma kara karfin kasa, don cimma manufofin siyasar kasar a harkokin waje.

Ya kara da cewa: Yawancin fitattun wakilan kafafen yada labarai na kasashen waje da dama sun fahimci mahimmancin zaben shugaban kasa, kuma sun zo Iran ne domin kallo da bayyana ma’auni na wannan lamari na siyasa mai matukar muhimmanci, da kuma matakin fitowar al’umma da kuma taka rawar da al’ummar Iran zasu taka a kan tubalin hangen nesa da kafa tarihi mai inganci a zabukan kasar.

Ya kuma fayyace cewa: ‘Yan jaridun kasashen waje 180 ne suka zo Iran domin bayar da rahotannin abubuwan da zasu faru da kuma yadda za a gudanar da zaben lamarin da ke nuna muhimmancin matsayi da rawar da Iran take da shi, da kuma ci gabanta a fagen yanki da na kasa da kasa, da kuma tasirin wannan zabe a fagen harkokin siyasar cikin gida da waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments