Jami’an Tsaron Mamaya Sun Kai Samame Kan Asibitin Holhol Da Birnin Khalil Na Falasdinu

Jami’an tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na musamman sun kai farmaki a asibitin Holhol tare da yin awungaba da wani maras lafiya Rahotonni sun bayyana

Jami’an tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na musamman sun kai farmaki a asibitin Holhol tare da yin awungaba da wani maras lafiya

Rahotonni sun bayyana cewa: A cikin tsakar dare, jami’an tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na musamman sun kai farmaki a asibitin gwamnatin Hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Falasdinawa na Holhol da ke lardin Khalil a kudancin gabar yammacin kogin Jordan, inda suka kama wani maras lafiya.

Daraktan asibitin, Salah Tamizi, ya ce: Ma’aikatan jinya sun yi mamakin lokacin da jami’an tsaron yahudawan sahayoniyya na musamman suka kawo samamen suna sanye da kayan fararen hula, inda suka kama wani maras lafiya da ke bukatar tsananin kula ta lafiya tare da yin awungaba da shi.

Daraktan ya kara da cewa: Farmakin da jami’an tsaro na musamman suka kai wa asibitin, wani mataki ne da ya saba wa dokokin kasa da kasa da kuma duk wasu yarjejeniyoyin kasa da kasa da suka haramta shiga asibitoci da cibiyoyin lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments