Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fara kaddamar da hare-hare daukan fansa kan kisan Isma’ila Haniyya musamman kan birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ta kada kararrawar gargadi kan yahudawan sahayoniyya su shige cikin ramuka karkashin kasa domin tsira daga hare-haren Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Idan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi gigin mayar da martani kan hare-haren daukan fansa kan kasarsa, to babu shakka zata fuskanci mayar da martani mafi tsanani.
Gidan talabijin na kasar Iran ya bayyana cewa: Hare-haren da aka kai kan haramtacciyar kasar Isra’ila, somin tabi ne, inda daga baya yahudawan sahayoniyya zasu fuskanci martani mafi gauni.
Rahotonni daga haramtacciyar kasar Isra’ila suna bayyana cewa: Babu kowa akan hanyoyin birnin Tel Aviv sakamakon hatsari hare-haren dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran.
A nata bangaren, Gwamnatin Joe Biden ta Amurka ta bada umarni ga sojojin Amurka da su kasance cikin Shirin kai dauki ga haramtacciyar kasar Isra’ila domin kalubalantar martanin Iran.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya watsa rahoton cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da rufe dukkanin filayen jiragen sama domin hare-haren da take fuskanta daga kasar Iran.
Kamar yadda tasha ta 13 ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto daga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila zata mayar da martani kan kasar Iran.