Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Watsi Da Maganar Cewa Duniya Tana Biyayya Ga Amurka

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Duk wanda yake tunanin cewa babu wani mataki da za a dauka ba tare da yardar Amurka

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Duk wanda yake tunanin cewa babu wani mataki da za a dauka ba tare da yardar Amurka ba, yana cikin rudu

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne a yau Talata a lokacin da ya karbi bakuncin dubban mutane daga larduna biyar na kasar Iran a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan sallar Idin Ghadir Khumj da kuma ci gaba da zama na goma sha hudu na zaben shugaban kasa. ya ce ci gaba da gudanar da siyasar Musulunci yana kara janyo yanke kauna a cikin zukatan kafirai.

An fara gudanar da wannan biki mai taken ‘yan uwantaka da jagoranci a safiyar yau Talata, a Husainiyar Imam Khumaini (a.s) da ke birnin Tehran babban birnin kasar, tare da halartar al’ummar lardunan Gilan ta tsakiya, Kohkiluyeh da Boyer Ahmad, Khorasan ta Arewa, iyalan shahidai, da kuma ma’aikatan habbaren Shahgaragh mai alfarma.

A cikin jawabinsa, Jagoran ya jaddada bukatar fitowa domin gudanar da zabe da kuma zaben wanda ya fi dacewa, sannan kuma ya fayyace cewa gagarumar fitowa zaben yana nuna daukakar tsarin Jamhuriyar Musulunci ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments