Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Duk wani mataki da za a dauka kan Iran da kuma bangaren gwagwarmaya, za a fuskanci kakkausan martani mai karfi
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Al’ummar Iran da jami’an kasar ba za su taba yin kasa a gwiwa ba wajen tunkarar girman kan duniya da kuma kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke tafiyar a kan tsarin rashin adalci a wannan duniya a yau, sannan kuma makiya su sani musamman Amurka da yahudawan sahayoniyya za su fuskanci martani mai zafi da tsanani.
A ci gaba da bukukuwan ranar yaki da masu girman kai da ranar dalibai a Jamhuriyar Musulunci ta Iran (wato ranar 13 ga watan Aban) a jiya Asabar aka gudanar da wata ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da dimbin daliban makarantu da jami’o’i na sassa daban-daban na kasar Iran a Husainiyar Imam Khumaini (r.a).
A yayin ganawar Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Jami’ai a Iran suna yin duk abin da ya dace wajen shirya al’ummar Iran wajen tunkarar girman kai, walau ta fuskar soja da makamai ko kuma ta fuskar siyasa, kuma jami’ai a Iran ba za su taɓa yin shakka ba, ta kowace hanya, don fuskantar girman kai na duniya da ke tafiyar da tsarin duniya a yau.