Jagora: Fitowa Domin Zaben Shugaban Kasa A Gobe Juma’a Yana Da Matukar Muhimmanci

Jagoran juyin musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  wanda ya gana da malaman jami’ar Shahid  Mutahhari a jiya Laraba d aake karatar yin zaben

Jagoran juyin musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  wanda ya gana da malaman jami’ar Shahid  Mutahhari a jiya Laraba d aake karatar yin zaben shugaban kasa zagaye na biyu, wanda zai kasance a gobe Juma’a, inda ya yi kira ga al’ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin yin zaben.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana fitowar mutane domin yin zaben a matsayin wani abin alfahari ga tsarin jamhuriyar musulunci ta Iran.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma kara da cewa; gwargwadon yadda za a gudanar da zabe mai nagarta, da yawan fitowa, tsarin musulunci na  Iran zai sami damar cimma manufofin da ya sanya a gaba.

Zaben na gobe dai za a yi shi ne a tsakanin ‘yan takara biyu da su ne; Mas’ud Fizishkiyan da kuma Sa’id Jalili da su ne su ka fi samun kuri’u mafi yawa a zagayen farko na zabe.

A zagayen farko na zabe, fiye da mutane miliyan 24 su ka kada kuri’unsu wanda aka shirya domin zabar wanda zai maye gurbin shahid Ibrahim Ra’is da ya yi hatsarin jirgin sama mai saukar Angulu a ranar 19 ga watan Mayu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments