Isra’ila Ta Sake Yin Wani Kisan Kiyashi A Yankin Rafah Da Ke Kudancin Gaza

Kafofin yada labarai a Gaza sun ce sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-haren sama fiye da 70. Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da

Kafofin yada labarai a Gaza sun ce sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-haren sama fiye da 70.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoton mutuwar mutum 32, tana mai cewa “an kai waɗanda suka mutun, wadanda akasarinsu yara da mata ne zuwa asibitoci cikin dare, saboda kisan kiyashin da ake ci gaba da yi”.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana kuma gwabza fada a yankin Rafah da ke kudancin kasar, inda dakarunta suka “kawar da ‘yan ta’adda da dama a hare-hare ta sama”.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga ƙungiyar ƙawance ta NATO ta ƙara matsa wa Firminisatan Isra’ila Benjamin Netanyahu lamba don tabbatar da cewa an samu tsagaita wuta da kuma shigar da kayan jin ƙai ba ƙwaƙƙautawa zuwa yankin Gaza da aka mamaye.

Erdogan ya zargi Netanyahu da jefa Isra’ila da ma duka ƙasashen yankin cikin haɗari saboda manufofinsa na mamaya da ganganci.

Ya kuma ƙara da cewa Turkiyya ba za ta amince da duk wata haɗaka tsakani NATO da Isra’ila ba har sai an shimfiɗa gamsasshen tsarin zaman lafiya a Falasɗinu.

“Matuƙar ba a shimfiɗa tabbatacce kuma dawwamammen tsarin zaman lafiya a Falasɗinu ba, to duk wani yunƙurin haɗaka da Isra’ila ba zai samu amincewar Turkiyya ba,” a cewar Erdogan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments