Isra’ila ta sake kashe wani adadi mai yawa na Falasdinawa a arewacin Gaza

Akalla karin Falasdinawa 27 ne Isra’ila ta kashe a hare-haren da ta kai a Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa

Akalla karin Falasdinawa 27 ne Isra’ila ta kashe a hare-haren da ta kai a Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 43,341, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 102,105 sun jikkata a harin da ake ci gaba da kaiwa.

“Sojojin Isra’ila sun kashe mutum 27 tare da jikkata wasu 86 a kisan gilla da aka yi wa iyalai hudu a cikin sa’o’i 24 da suka wuce,” in ji ma’aikatar.

A daya bangaren kuma Rundunar Sojin Isra’ila ta bayyana cewa wani sojanta ya halaka a arewacin Gaza bayan gurneti ta fashe a hannunsa.

Kafar watsa labarai ta Channel 13 ta Isra’ila ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar haka kuma ana gudanar da bincike domin gano dalilin da ya jawo fashewar gurnetin.

Mutuwar sojin na Isra’ila ta sa adadin sojin ƙasar da suka mutu tun bayan soma yaƙin Gaza zuwa 780, kamar yadda ƙididdigar sojin ƙasar ta nuna. Daga cikin waɗannan, mutum 368 sun mutu ne a yayin da suke kai farmaki ta ƙasa a cikin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments