Isra’ila Ta Kashe Falastinawa 40 A Wasu Hare-Hare Kan Zirin Gaza

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hari kan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a yankin kudancin zirin Gaza da bama-bamai da Amurka ta samar da

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hari kan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a yankin kudancin zirin Gaza da bama-bamai da Amurka ta samar da suka kai nauyin ton 2,000, inda suka kashe fararen hula akalla 40 galibi mata da kananan yara.

Kimanin wasu 60 ne suka jikkata a wani harin da aka kai a wani yanki da sojojin Isra’ila suka ayyana a matsayin “yankin jin kai” a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Mawasi da ke birnin Khan Younis a ranar Talata.

Sojojin yahudawan sun yi da’awar cewa sun kai hari ne kan mambobin kungiyar gwagwarmayar Hamas, sai Hamas ta yi watsi da wannan ikirari, inda ta tabbatar da cewa babu daya daga cikin mayakan kungiyar a wurin alokacin da Isra’ila ta kaddamar da harin .

Bayanin na Hamas ya kara da cewa, dukkanin mutanen da Isra’ila ta kashe ko ta jikkata a wurin fararen hula mata da kanan yara.

Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba 2023 ne Isra’ila ta fara aiwatar da kisan kare dangi a kan al’ummar falastinu da sunan yaki da Hama a gaza, da kuma sauran Falastinawa ‘yan gwagwarmaya, inda ya zuwa yanzu, kusan Falasdinawa 41,000 ne suka yi shahada, tare da jikkata wasu fiye da 94,800 a munanan hare-haren kisan kare dangi na Isra’ila  a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments