A zaman da suka gudanar Wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da kisan gillar da Isra’ila ta yi wa shugaban ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran babban birnin Iran, yayin da wakilan dindindin na Amurka da Birtaniya suka zargi Iran da janyo rashin zaman lafiya a yankin.
A ranar Labara ne Majalisar ta kira wani zaman gaggawa kan kisan gillar da aka yi wa Haniyeh bisa buƙatar Iran inda ƙasashen Rasha da Aljeriya da kuma China suka yi maraba da hakan.
Da yake jawabi a wajen taron, jakadan China Fu Cong ya ce, ƙasarsa ta yi kakkausar suka ga kisan gillar da aka yi wa Haniyeh.
Kazalika wakilin Aljeriya a MDD Amar Bendjama ya ce: “Muna kan hanyar zuwa ga bala’i,” yana mai cewa harin Isra’ila wani “ta’addanci ne” wanda ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma iko da ‘yancin Iran.
”Wannan ba wai hari ne kan mutum ɗaya ba, kazamin hari ne kan tushen dangantakar diflomasiyya da take ikon ƙasa da kuma ƙa’idojin da ke ingiza tsarinmu na duniya, ” kamar yadda ya bayya.