Islami: Bayanin IAEA Ya Tabbatar Da Cewa Shirin Iran Na Nukiliya Bai Saba Wa Kaida Ba

Parstoday- Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya bayyana cewa, kasashe masu girman kai da yahudawan sahyuniya suna da’awar cewa Iran na da shirin nukiliya

Parstoday- Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya bayyana cewa, kasashe masu girman kai da yahudawan sahyuniya suna da’awar cewa Iran na da shirin nukiliya na sirri da ake gudanarwa a boye, ya ce, bayanin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, ya tabbatar da cewa babu wani abu na kauce hanya a shirin nukiliyar Iran.

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Mohammad Islami ya bayyana cewa: Sama da shekaru 20 ne aka bude shafin takaddama kan shirin Nukiliya na  Iran, kuma gwamnatoci masu girman kai da yahudawan sahyoniya suna ikirarin cewa Iran tana aiwatar da wani shiri na nukilioya a boye, da nufin ganin sun yi amfani da hakan wajen kara matsala a kan kasar ta Iran.

Islami ya fayyace: Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta sanar da cewa babu wata karkata a shirin nukiliyar Iran, wanda hakan ke nufin cewa dukkanin matakan da ake dauka kan Iranm matakai ne na siyasa, sakamakon ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran da sauran manyan kasashen duniya.

Islami ya kara da cewa: Iran ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta dangane da wannan yarjejeniyaa, amma kasashen Turai uku (Faransa, Jamus da Ingila) da Amurka sun dauki matsaya guda ta yin watsi da wanann yarjejeniya, ta hanyar kin aiwatar da abubuwan da ta kunsa, wadanda suka rattaba hannu a kansu.

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya bayyana cewa: lokaci ya wuce hukumar IAEa za ta ci gaba da zama kar kashin manufofin siyasar wasu kasashe, a maimakon hakan wajibi ne a kanta ta ci gaba da kasancewa  amatsayin hukuma mai cikakken ‘yanci da kuma gudanar da ayyukanta bisa ilimi da kwarewa, ba bisa manufofin siyasar wasu kasashe ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments