Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya bayyana aniyar iran na aiki da diflomasiya don tabbatar da zaman lafiya da tsaro, sai dai ya bayyana afili cewa harkokin diflomasiya ba zai hana iran ta kare kanta daga duk wata barazana ba
Babban jami’in yayi wannan bayanin ne a lokacin ganawarsa da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Poland da ya kawo ziyara kasar iran, kuma ya danganta rashin tsaro dake faruwa a yanki da mashigar Hurmuz da ayyukan ta’addancin da Amurka da isra’ila ke yi
Hakazalika ya soki hadin guiwa ko rashin daukar mataki da wasu kasashen turai suka yi dangane da harin soji da aka kai wa iran, ya jaddada cewa dukkan kasashe ciki har da kasashen turai dole ne mu dauki ginshikin matsayi ta hanyar yin tir da hari da kuma laifukan yaki da aka aikata a lokacin yakin