Iran : Yawan Fitowar Masu Kada Kuri’a Zai Zame Wa Kasar Abin Alfahari_Jagora

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce yawan fitowar masu kada kuri’a a zaben shugaban kasar da ke tafe

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce yawan fitowar masu kada kuri’a a zaben shugaban kasar da ke tafe zai zame wa kasar abin alfahari da kuma taimakawa kasar wajen kawar da makiyanta.

Jagoran ya bayyana hakan ne yau Talata a wani jawabi ga dubban Iraniyawa daga lardunan Tehran, Gilan, Kohgiluyeh da Boyer-Ahmad, Markazi da kuma Khorisan ta Arewa, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Eid al-Ghadir a gabanin zaben shugaban kasar da za’a gudanar a ranar Juma’a.

Zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 28 ga watan Yuni, tamkar wani gwaji ne ga al’ummar Iran, wanda kuma ya fi mahimmanci fiye da koda yaushe inji jagoran.

A ranar Juma’a mai zuwa ne al’ummar Iran za su kada kuri’a domin zaben shugaban kasa daga cikin ‘yan takara shida da ke neman maye gurbin marigayi shugaba Ebrahim Raeisi.

Har ila yau, Ayatullah Khamenei ya bayyana fatansa na cewa zaben zai zama abin alfahari ga al’ummar Iran ta hanyar zabar ‘dan takara mafi cancanta.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa : Daya daga cikin abubuwan da ke ba wa Jamhuriyar Musulunci damar cin galaba kan makiyanta shi ne zaben.

Daga nan sai ya shawarci jama’a da su fito dafifi don kada kuri’a a zaben domin domin tsone idon makiya da tabbatar da tsarin Musulunci da kasar ke akansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments